Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe 5 na tsakiyar Asiya suna da ta cewa sama da Amurka kan halin Xinjiang
2020-01-01 15:28:32        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce kasashen tsakiyar Asiya 5, masu makwaftaka da jihar Xinjiang ta kasar Sin, su ne suka fi dacewa da fadin ainihin yanayin da jihar ke ciki, sabanin Amurka.

Kalaman na Geng Shuanag na zuwa ne, bayan da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa, sakataren wajen kasar Mike Pompeo, zai ziyarci kasashen Kazakhstan, da Uzbekistan, da wasu kasashen na daban cikin farkon watan da muke ciki, kana zai halarci taron ministocin wajen kasashen Asiya 5 tare da Amurka ko (C5 + 1) a Turance, taron da zai gudana a birnin Tashkent.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ta ce, a yayin taron, Mr. Pompeo zai tattauna batun jihar Xinjiang. A cewar ma'aikatar, Amurka ba ta ga wani abun a zo a gani na ci gaba, da aka samu a yanayin jihar ta Xinjiang ba.

Game da hakan, Geng Shuang ya ce idan aka bibiyi abubuwan da suka wakana, yayin taron ministocin wajen kasashen C5+1 da ya gudana a watan Satumbar shekarar da ta gabata, Amurka ta yi kokarin shafawa Sin kashin kaji, tare da haifar da wani yamutsi, ko da yake hakar ta bai cimma ruwa ba. Jami'in ya ce ko da Amurka ta maimaita irin wannan dabara a yanzu, ba za ta cimma nasara ba.

Geng Shuang ya kuma jaddada matsayar gwamnatoci da al'ummun kasashen tsakiyar Asiya, na kulla makwaftaka, da kawance, da abota cikin kyakkyawan yanayi tare da Sin, kana da yakar 'yan ta'adda, da masu kawo kasa baraka da kuma masu tsattsauren ra'ayi.

Ya ce Sin a tsaye take kan wannan manufa, kuma dukkanin wani mataki na kokarin shafa mata bakin fenti, da rura wutar wariya, da tozarta ta a idanun duniya ba zai yi nasara ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China