Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin baitulmalin Amurka ya sanar da kaso kusa da sifili a matsayin mizanin kudin ruwa zuwa shekarar 2022
2020-06-11 10:11:47        cri
Ofishin baitulmalin Amurka, ya sanar a jiya Laraba cewa, mizanin kudin ruwan bankuna ba zai canza ba, a kalla zuwa karshen shekarar 2022, a gabar da darajar kudin ruwan ke kusantar sifili, sakamakon komadar tattalin arziki da cutar COVID-19 ta haifar.

Kwamiti mai lura da kasuwanni na baitulmalin Amurka, wanda ke tsara manufofin da ofishin ke aiwatarwa, ya fitar da wata sanarwa bayan taron sa na yini biyu, inda a cikinta ya ce, kalubalen kiwon lafiya da ake fama da su a yanzu haka, za su yi matukar tasiri ga hada hadar tattalin arzikin kasar, da fannin ayyukan yi, da hauhawar farashi na gajeren lokaci. Kaza lika hakan zai haifar da barazanar shiga matsalolin tattalin arziki na matsakaicin lokaci.

Sanarwar ta kara da cewa, bisa wannan yanayi, kwamitin ya amince da tsayar da mizanin kudin ruwa a fannin hada hadar kudaden kasar, tsakanin kaso 0 zuwa 0.25 bisa dari.

Da yake tsokaci kan yanayin da ake ciki, yayin wani taro ta kafar bidiyo da ya gudana a jiya Laraba, shugaban bankin ajiyar na Amurka Jerome Powell, ya ce yaduwar cutar COVID-19, da matakai na wajibi da aka dauka domin dakile ta, sun mayar da hannun agogo baya a fannin hada hadar tattalin arziki, sun kuma kara fadada matsalar rashin ayyukan yi tsakanin al'ummar kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China