Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai yiwuwar gurfanar da wani dan sandan Atlanta bisa harbe wani bakar fata
2020-06-15 14:14:09        cri

Mai yiwuwa a yanke shawara a tsakiyar makon nan, kan gurfanar da wani dan sanda da ya harbe wani bakar fata a ranar Juma'a, a Atlantan Amurka.

Sanarwar da lauyan gundumar Fulton, Paul Howard ya fitar a jiya, ta ce akwai abubuwan da ake bukatar tabbatarwa kafin yanke shawarar, yana mai cewa, yana fatan sanar da shawarar da aka yanke ya zuwa tsakiyan mako.

An harbe Rayshard Brooks, baAmurke bakar fata, mai shekaru 27 ne bayan an tura 'yan sanda amsa kiran da aka yi musu cewar barci a wajen wani dakin sayar da abinci da ba a sauka a mota.

'Yan sanda sun ce sun yi kokarin kama Brooks, bayan ya ki a yi masa gwajin maye, wanda ya kai su ga kokawa. 'Yan sanda sun yi ikirarin cewa, yayin da ya ke turjewa, ya dauki bindigar lantarki na dan sanda tare da tserewa.

Bidiyon da aka dauka a wurin, ya nuna Brooks na nuna bindigar ga 'yan sanda, kafin a harbe shi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China