Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta aike da kaso na biyu na tallafin yaki da COVID-19 ga Zimbabwe
2020-06-12 13:49:21        cri

A jiya Alhamis gwamnatin kasar Sin ta aike da kashi na biyu na tallafin kayayyakin kiwon lafiya don yaki da annobar COVID-19 ga kasar Zimbabwe yayin da a 'yan makonnin nan ake samun karuwar adadin masu kamuwa da cutar a kasar ta kudancin Afrika.

Kashi na biyu na kayan tallafin sun hada da takunkumin fuska da jami'an lafiya ke amfani da su kimanin 165,000, da rigunan ba da kariya wato PPE kimanin 25,000.

Jakadan kasar Sin a Zimbabwe Guo Shaochun, shi ne ya mika gudunmawar kayayyakin ga shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, a lokacin bikin mika kayan da aka gudanar a fadar gwamnatin kasar.

A jawabin da ya gabatar lokacin bikin, jakadan na Sin ya ce, wannan gudunmowa ta kara nuna karfin abotar dake tsakanin bangarorin biyu. Bayan da gwamnatin Sin ta jagoranci bayar da tallafin, ragowar bangarori kamar bangaren sojojin kasar Sin, da kungiyoyin 'yan kasuwa da daidaikun jama'a dukkansu sun bi sahun gwamnatin, inda suke mika tallafinsu ga kananan hukumomi, da asibitoci, da makarantu, da marasa galihu.

Yayin da yake karbar tallafin, Mnangagwa ya bayyana godiyar da Zimbabwe ta nuna ga taimakon da Sin ke ci gaba da baiwa kasarsa, ya ce tallafin yana da matukar muhimmanci wajen taimakawa kasar yaki da yaduwar annobar a kasar.

Mnangagwa ya ce, wannan taimako da yin hadin gwiwar za su taimaka matuka ga irin kokarin da kasar Zimbabwe ke yi a yaki da annobar kuma zai taimakawa jami'an lafiyar kasar cikakkiyar kariya yayin da suke gudanar da ayyukansu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China