Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sudan ta bayyana shirinta na zurfafa hadin gwiwa da Sin a fannoni da dama
2020-06-15 09:49:39        cri

Shugaban kwamitin mulkin riko na kasar Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce a shirye kasarsa ta ke, ta yi koyi da nasarorin da kasar Sin ta samu wajen yaki da kandagarkin cutar COVID-19, da zurfafa hadin gwiwa da musaya a fannonin kiwon lafiya da kandagarkin annoba da ciyar da huldar kasashen gaba.

Da yake ganawa da jakadan Sin a Sudan, Ma Xinmin, Burhan ya godewa gwamnatin kasar Sin bisa taimakon da ta ba jami'an kiwon lafiya na kasar. Ya kuma jaddada cewa Sudan na daukar kasar Sin a matsayin abokiyar hulda mafi aminci da za a iya dogaro da ita, yana mai gode mata da irin taimakon da ta dade tana ba kasarsa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China