Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya za ta mayar da kamfanonin yawon bude ido zuwa kafofin watsa labarai na zamani
2020-06-17 10:24:53        cri
Kasar Kenya za ta gudanar da gagarumin sauyi a fannin yawon bude ido, inda za ta sauya tsarin talabijin da fannin jarida zuwa fannin kafofin watsa labarai na zamani, kamfanin wasanni na kasar ne ya sanar da hakan.

Kamfanin wasannin ya ce, lokaci ya yi da kasuwannin yada labarai na zamani suke matukar samun karbuwa musamman bisa yadda annobar COVID-19 ta haifar da koma baya a fannin kamfanonin yawon bude ido a watanni uku da suka gabata.

Betty Radier, babban jami'in hukumar yawon bude ido na kasar Kenya (KTB) ya ce, kamfanin yana amfani da kafafen sada zumunta na zamani wajen shirya matakan saukaka zirga-zirga sakamakon cutar COVID-19 domin baiwa masu ziyara damar tantance wuraren da suke son ziyarta a kan lokaci.

Damian Cook, manajan daraktan sashen aikin yawon bude ido na zamani, ya ce, amfani da hanyoyin sadarwar na zamani yana taimakawa wajen fahimtar muhimman wurare da ayyukan da ake gudanarwa da muhimman bayanai da mutane ke matukar bukatarsu a wadannan wurare. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China