Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 285 a Kenya
2020-05-28 11:07:56        cri

Kimanin mutane 285 ambalisar ruwa ta hallaka, kana wasu mutanen 810,655 sun gamu da iftila'in zaftarewar kasa, sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu a sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar Kenya.

Eugene Wamalwa, sakataren gwamnatin kasar, ya shedawa 'yan jaridu a Nairobi cewa, ambaliyar ruwa da kuma tumbatsar kogi da tafkuna sun haifar da mummunar illa ga kasar.

Ya yi gargadin cewa, akwai yiwuwar za'a ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwan a gabar tekun yammacin kasar Kenya yayin da ake hasashen samun karuwar mamakon ruwan sama a watan Yuni.

Jami'in ya ce, gwamnati za ta ci gaba da taimakawa iyalan da bala'in ya shafa wajen samar musu da tallafin kayan abinci da sauran muhimman kayayyakin bukatu, ya kara da cewa, lokaci ya yi da ya kamata jama'ar kasar Kenya su dora muhimmanci kan gargadin hasashen yanayi domin gujewa fuskantar hasarar rayuka a nan gaba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China