Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya za ta ci gaba da gwajin kwayoyin dake kara kuzari ga 'yan wasan  Olympic duk da barazar annoba
2020-05-17 15:50:57        cri
Kasar Kenya ta kebe kudin kasar shillings miliyan 17 kwatankwacin dala 170,000, domin yaki da masu shan kwayoyin dake kara kuzari a kungiyar 'yan wasa a kasar dake shirye-shiryen shiga gasar wasannin Olympic na Tokyo wadda aka dage.

Babban jami'in hukumar yaki da ta'ammali da kwayoyin kara kuzari ga 'yan wasa ta Kenya wato (Adak), Japhter Rugut, ya ce wannan yana daga cikin irin shirye-shiryen da ake yi na yaki da shan kwayoyin dake kara kuzari ga 'yan wasa, wanda ya yi sanadiyyar jefa kasar cikin fuskantar suka bayan samun adadi mai yawa na 'yan wasan wadanda gwajin da aka yi musu ya nuna suna ta'ammali da kwayoyin kara kuzarin 'yan wasa, lamarin da ya sa aka haramtawa 'yan wasan kasar su 60 shiga gasanni.

Rugut ya ce, sun ware kudaden yaki da masu shan kwayoyin kara kuzarin 'yan wasan kuma suna samun nasara a yakin da suke yi, ko da yake, ba lallai ne a kawar da matsalar baki daya ba. A cewarsa sun ware dala 170,000 ga shirin na wasannin Olympic yayin da suka samar da dala miliyan 2.6 domin shirin tinkarar wasannin motsa jiki ta duniya ta Doha tun a shekarar da ta gabata.

Kenya, tare da kasashen Habasha, Ukraine, Belarus, Najeriya, da Bahrain, hukumar shirya wasannin ta duniya ta saka su a rukunin A, wata kila saboda an samu 'yan wasan nasu da aikata laifuka ne.

Hakan na nufin cewa, gabanin wasannin Championship ko Olympics na duniya tilas ne wadannan rukuni su gudanar da gwajin kafin samun damar shiga wasannin Olympics. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China