![]() |
|
2020-01-29 16:09:38 cri |
Rahoton da asusun ya fitar a jiya, ya ce karuwar rikici a yankin tsakiyar Sahel na Afrika, na nufin kusan yara miliyan 5 za su bukaci agajin gaggawa a bana, adadin da ya karu kwatankwacin miliyan 4.3 na 2019.
A cewar rahoton asusun, ana kai wa yara hari da sace su ko horar da su a matsayin mayakan kungiyoyin saboda karuwar rikici da rashin tsaro a Burkina Faso da Mali da Niger. Ya kara da cewa, tun daga farawar rikicin a shekarar 2019, ya tilastawa yara sama da 670,000 a fadin yankin tserewa daga gidajensu.
UNICEF na neman dala miliyan 208 domin gudanar da ayyukan da take yi a yanzu, inda take aiki da abokan huldarta a fannonin bada kariya da samar da ilimi da kiwon lafiya da abinci mai gina jiki da ruwa da tsafta. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China