Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Tashin hankali ya raba yara miliyan 1.9 daga makarantu a tsaki da yammacin Afrika
2019-08-24 16:05:33        cri
Sama da kananan yara miliyan 1.9 daga wasu kasashe 8 na yammaci da tsakiyar Afrika rikici ya tilastawa kauracewa makarantunsu, kakakin MDD ce ta bayyana hakan a jiya Juma'a.

Eri Kaneko, mai magana da yawun sakatare janar na MDD Antonio Guterres, tace rahoton asusun tallafawa ilimin kananan yara na MDD (UNICEF), ya bayyana cewa, kimanin makarantu 9,272 ne aka rufe a kasashen Burkina Faso, Kamaru, Chad, Afrika ta tsakiya, demokaradiyyar Kongo, Mali, Nijer da Najeriya, sakamakon matsalolin tabarbarewar tsaro.

Tace adadin makarantun da aka rufe su a watan Yuni sun ninka yawan wadanda aka rufe a karshen shekarar 2017 har sau uku.

A cikin rahoton, hukumar UNICEF da abokan huldarta sun bukaci gwamnatoci, da sojoji, da al'ummar kasa da kasa, dasu hada gwiwa wajen daukar matakan dakile dukkan barazanar da suka shafi makarantu, da dalibai, da malamai, da sauran jami'an dake kula da harkokin makarantu a shiyyar tsakiya da yammacin Afrika.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China