Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin kasar Sin na samun farfadowa
2020-06-15 20:49:23        cri

 

Hukumar kididdigar kasar Sin ta bayar da alkaluma, game da yadda aka gudanar da tattalin arzikin kasar a watan Mayu, inda aka gano cewa, ma'aunin muhimman alkaluman na samun kyautatuwa, kuma tattalin arzikin kasar na ci gaba da samun farfadowa. Bisa matsin lamba da kasar Sin ke fuskanta a cikin gida da waje, tattalin arzikin kasar na cike da karfi na tinkarar matsalar da ke kasancewa cikin gajeren lokaci, da kuma kara samun bunkasuwa a nan gaba.

Bisa yanayin da ake ciki na dakile annobar COVID-19, kasar Sin tana girmama tsarin ci gaban tattalin arziki, kuma ta daidaita burin ci gaba bisa hakikanin halin da ake ciki a kan lokaci, kana da ba da tabbaci ga samar da guraban aikin yi ga jama'a, da kiyaye zaman rayuwar jama'a, da kiyaye kasuwanni da dai sauransu, a matsayin manyan manufofin na tinkarar duk wani hadari da ka iya kunno kai.

Yanzu dai, manufofin sun soma yin amfani, ba kawai wajen tabbatar da tushen tattalin arziki ba, har ma sun tabbatar da hasashen da aka yi kan kasuwanni.

 

 

Baya ga haka, bisa alkaluman da aka bayar kan tattalin arzikin kasar Sin a watan Mayu, an kuma bullo da wasu abubuwa masu kyau dake daukar hankalinmu.

Da farko, ana ta samun kyautatuwa a fannin sayayya. Sakamakon dakile annobar yadda ya kamata, kasuwannin sayayya na samun kyautatuwa a cikin watanni uku a jere. Na biyu, sana'ar sabbin fasahohi na zamani, na kasancewa ginshiki na bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin.

Kamfanin KPMG dake kasar Sin, ya bayar da rahoto game da tattalin arzikin kasar Sin a cikin watanni 6 na farkon shekarar bana, inda ta nuna cewa, bisa kokarin kasar Sin na kara kiyaye ikon mallakar fasaha, kasar za ta kara janyo masu cinikayyar waje, su zuba jari kan fasahohin zamani a kasar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China