Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin kasar Sin na kara murmurewa
2020-04-17 22:01:34        cri

Alkaluman hukumar kididdiga ta kasar Sin sun nuna cewa, a farkon watanni ukun bana, yawan GDPn kasar ya zarta Yuan triliyan 20, wanda ya ragu da kaso 6.8% bisa makamancin lokacin bara.

Wannan ba abun mamaki ba ne. Saboda a farkon watanni ukun shekara da muke ciki, kasar Sin ta fuskanci babban kalubale a fannin yaduwar cutar mashako ta COVID-19, kuma abu mai muhimamnci shi ne ceto rayukan jama'a. A sabili da haka, gwamnatin kasar take daukar kwararan matakan kandagarkin yaduwar cutar, da takaita zirga-zirga, da kuma dakatar da saurin raya tattalin arziki, al'amarin da ya sa kasar ta iya shawo kan cutar cikin wani kankanin lokaci, amma hakan ya shafi saurin ci gaban tattalin arzikin kasar.

Cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa a fadin duniya, kuma akwai kasashe da dama wadanda suka rage hasashen da suka yi na habakar tattalin arzikinsu. Kasar Sin ma ba za ta iya kebe kanta daga tawayar tattalin arzikin da duniya ke fuskanta ba, wato ita ma tana fuskantar matsalar koma-bayan tattalin arziki.

Abun lura a nan shi ne, a watanni biyu da suka shige, a yayin da take kokarin hana yaduwar cutar, a sa'i daya, Sin tana himmatuwa wajen farfado da tattalin arzikinta ta hanyar sake dawo da ayyukan kere-kere, kuma kwalliya ta riga ta biya kudin sabulu. Cutar na kara samun sauki a kasar, har ma tattalin arziki gami da zaman rayuwar al'umma duk suna ta murmurewa cikin sauri. Kana, gwamnatin kasar na kokarin samar da guraban ayyukan yi da kuma tabbatar da farashin kaya, abun da ya kara inganta zaman rayuwar al'ummar kasar na yau da kullum.

A fili yake cewa, illolin da cutar COVID-19 ke haifarwa ba za su canja makomar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba, wannan ya sa, kasashen duniya ke ci gaba da nuna imani ga kyakkyawar makomar kasuwannin kasar.

Asusun bada lamunin duniya wato IMF ya yi hasashen cewa, Sin na daya daga cikin kasashen duniya kalilan wadanda za su samu ci gaban tattalin arziki a bana, kana, asusun ya yi kiyasin cewa, yawan karuwar tattalin arzikin kasar a shekarar 2021 zai kai kaso 9.2%, abin da ya sanya ta zama kasar da tattalin arzikinta ke farfadawo cikin sauri tsakanin kasashen G20.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China