Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba za a hana bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba ba
2020-02-07 19:43:58        cri

Yau Jumma'a shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, inda ya jaddada cewa, kasar Sin tana da imani da kwarewa wajen samun nasarar yaki da annobar cutar numfashi da ta bulla a kasar, kuma wannan annoba ba za ta hana bunkasuwar tattalin arzikin kasar a nan gaba ba.

Illar da annobar za ta haifarwa wa tattalin arzikin kasar Sin ta danganta da yadda ake yaki da annobar. Yanzu haka an shiga muhimmin mataki na yaki da annobar. Gwamnatin Sin ta fito da wasu matakan hada-hadar kudi, a kokarin ba da tabbaci ga yaki da annobar da kuma maido da ayyuka da inganta zaman rayuwar jama'a a sassa daban daban na kasar.

Ba kawai kasar Sin za ta cimma nasarar yaki da annobar ba, hatta ma tana da kwarewar ci gaba da raya tattalin arzikinta a nan gaba. Za ta kuma ci gaba da kara kuzari kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China