Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me ya sa kasar Sin ta ci gaba da kasancewa jagoran bunkasuwar tattalin arzikin duniya
2020-01-17 20:40:23        cri

A yau Juma'a ne babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, ya fitar da wani sharhi mai taken "Me ya sa kasar Sin ta ci gaba da kasancewa jagoran bunkasuwar tattalin arzikin duniya".

Sharhin ya ce, hukumar kididdiga ta kasar Sin, ta sanar a yau cewa, yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasar a shekarar 2019 ya wuce RMB triliyan 99, wato ya bunkasa da kaso 6.1 cikin 100, wannan adadi ya yi daidai da abin da gwamnati ta yi hasashen cimmawa, ana iya cewa kasar din na ci gaba da samun saurin bunkasar tattalin arziki. A yanayin da ake ciki na kara fuskantar kalubaloli a cikin gida da na waje, Sin ta ci gaba da kasancewa a sahun gaba a wannan fanni.

Sharhin ya kuma nuna cewa, irin nasarar da kasar Sin ta cimma babbar kasuwarta, da kuma manufofi masu dacewa da ta kaddamar, ciki har da inganta yin kwaskwarima kan kamfanoni mallakar gwamnati, da kyautata muhallin gudanar da cinikayya da dai sauransu. Ban da wannan kuma, a cikin shekarar da ta wuce, jerin matakan da kasar Sin ta dauka na kara bude kofa ga ketare sun kara imanin masu zuba jari na kasa da kasa kan tattalin arzikin kasar, haka kuma dangantakar tsakanin kasar ta Sin da kasa da kasa ta karfafa.

Baya ga haka, sharhin ya kuma jaddada cewa, a shekarar 2020, kasar Sin za ta ci gaba da dora muhimmanci kan neman ci gaba mai inganci, da bada tabbacin gudanar tattalin arziki yadda ya kamata, kana da bada tabbaci wajen kafa zaman al'umma mai matsakaicin karfi, da cimma nasara kan shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13, ta yadda za ta ci gaba da kasancewa jagoran tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China