Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gano gawarwaki 82 bayan hare-haren da kungiyar BH ta kai arewa maso gabashin Nijeriya
2020-06-15 09:36:26        cri

Kimanin gawarwaki 82 aka gano kawo yanzu, bayan hare-hare 4 da ake zargin kungiyar Boko Haram da kai wa wasu wurare 3 na jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Daga cikin gawarwakin da aka gano a ranar Asabar, har da na mayakan kungiyar da fararen hula da sojoji.

Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya, rundunar sojin kasar ta ce mayakan BH 20 kadai sojoji suka kashe yayin da suke mayar da martani kan harin da aka kai garin Monguno, daya daga cikin wuraren da aka kai wa hari a cikin karshen mako.

Rundunar sojin ta ce, mayakan sun yi kokarin kutsawa garin, sai dai dakarun sun karya lagonsu. Ta ce an kama wasu daga cikin maharan tare da makamansu, ciki har da motocin yaki 4 da aka lalata.

Kafofin watsa labaru da majiyoyi daga wurin, ciki har da masu ayyukan jin kai, sun tabbatar da kisan sojoji 20 a lokacin da suke kokarin dakile yunkurin harin.

A cewar wani babban hafsan soji, an kuma kashe fararen hula 42 a Gubio da Nganzai, wasu wurare 2 da suka fuskanci mummumnan harin na kungiyar BH. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China