Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan bindiga sun kashe mutane 18 a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya
2020-06-11 09:25:58        cri

Yan sandan Najeriya sun sanar a ranar Laraba cewa, an tabbatar da mutuwar mutane 18, sannan wasu mutane 22 sun samu raunuka bayan wani hari da 'yan bindiga suka kaddamar a shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Maharan, wadanda yawansu ya tasamma 200, kuma hukumomi sun yi amannan barayi ne, sun afkawa kauyen Kabiso dake karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, da nufin satar abinci, amma mazauna kauyen sun katse musu hanzari, a cewar hukumar 'yan sandan jihar.

Gambo Isah, kakakin hukumar 'yan sandan jihar, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, 'yan bindigar sun bude wuta kan jama'ar kauyen yayin da mutanen suka yi kokarin hana su satar kayan abincin.

Isah ya ce, 'yan bindigar sun bude wuta kan mutane. Kuma ya zuwa ranar Talata, an ba da rahoton mutuwar mutane 14 yayin da aka kai mutane 26 asibiti sakamakon samun raunuka, ya kara da cewa, wasu karin mutanen hudu sun mutu a lokacin da ake ba su kulawa a asibiti.

Yankin arewa maso yammacin Najeriya yana fama da matsalar tashe tashen hankalu a shekaru da dama. Da suka hada da matsalar barayi, da masu garkuwar da mutane don neman kudin fansa, da sauran ayyukan bata gari, wadanda ke neman zama ruwan dare a shiyyar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China