Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta amince da hukunci mai tsanani kan masu fyade
2020-06-12 09:54:32        cri

Gwamnatin Najeriya ta amince da hukunci mai tsanani kan mutanen da suka aikata fyade da cin zarafin kananan yara kamar yadda ministar harkokin mata ta kasar ta gabatar, inda ta bayyana karuwar ayyukan fyade da cewar abin takaici ne.

Pauline Tallen, ministar al'amurran mata ta Najeriya, ta fadawa 'yan jaridu a Abuja jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar kasar a ranar Laraba cewa, gwamnati ta amince a zartar da hukunci mai tsanani kan mutanen da suka aikata laifin yin fyade.

A cewar ministar, majalisar ta yi nuni da cewa, dama akwai dokar da ta shafi hukunta masu aikita laifin cin zarafi wato VAPPA, a takaice, ta shekarar 2015, wacce aka amince za'a yi amfani da dokar a matakan jihohin kasar domin hukunta masu aikita laifin fyade daidai da laifin da suka aikata.

Masu fafutuka sun sha yin kiraye kiraye ga hukumomin Najeriya da su zartar da tsattsauran hukunci kan masu aikita fyade ta hanyar tsaurara dokokin da ake da su a halin yanzu don hukunta masu laifin.

A ranar 5 ga watan Yuni, gamayyar kungiyoyin fararen hula da na kare hakkin dan adam sun gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin kasar da jihar Legas, inda suka nemi a aiwatar da dokar ta baci kan masu aikata laifin cin zarafi da keta hurumin jama'a a Najeriyar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China