Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Nijeriya ya bukaci sojojin kasar su matse kaimi a yaki da BH
2020-06-12 10:00:41        cri

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana kaduwa da kisan mutane akalla 81 da ake zargin mayakan Boko Haram da aikatawa a yankin arewa maso gabashin kasar, yana mai kira ga sojojin kasar su matse kaimi a yaki da kungiyar.

Muhammadu Buhari, ya bukaci rundunonin sojin kasar, su ci gaba da dorawa kan jerin nasarorin da suka samu kan 'yan ta'addan, domin cin galaba kansu da ceto mutane da shanun da suka sace.

Ya ce zuwan kashe-kashen a wannan lokaci abun kaduwa ne, ganin cewa ba a dade da fita daga watan Ramadhan da kuma yin sallah ba, kana kasar na shirin bikin ranar demokradiyya.

Kakakin rundunar sojin kasar, Sagir Musa, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, dakarun za su bibiya tare da kamawa ko kashe dukkan 'yan ta'adda da 'yan fashi da sauran abokan huldarsu a jihohin Borno da Katsina da Sokoto dake arewacin kasar.

Mayakan da ake zargin 'yan kungiyar BH ne, sun kuma sace mutane 7 a lokacin da suka kai hari kauyen Faduma Koloram dake karamar hukumar Gubio na jihar Borno a ranar Talata. Haka zalika, wasu karin mutane 13 sun ji rauni, baya ga gidaje da dama da suka kona tare da sace daruruwan shanu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China