Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan al-Shabab sun kashe dan sandan sa kai a arewacin Kenya
2020-06-15 09:19:47        cri

Mayakan kungiyar al-Shabab sun kashe wani jami'in dan sanda dake aikin sa kai a kasar Kenya, da safiyar jiya Lahadi, a garin Mandera dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Kwamandan 'yan sandan yankin Rono Bunei, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an kashe dan kungiyar daya, a lokacin da suka kai samame garin, bayan kokarin da suka yi na lalata wata hasumiyar sadarwa, sai dai sun fuskanci turjiya daga jami'an tsaron dake garin.

Rono Bunei ya kara da cewa, bayan sun gaza cimma nasarar lalata hasumiyar, sai suka dauke dan sandan mai suna Abdi Maalim. Da farfo an dauka ya bata, sai daga bisani, aka samu gawarsa a wani wuri da ba shi da nisa da garin. 'Yan sanda sun ce maharan su tafi da bindigarsa.

Har ila yau, kwamandan ya ce jami'an tsaron sun kashe dan kungiyar al-Shabab 1, kuma sun yi imanin cewa, ragowar sun tsere da raunika.

Shi ma kwamandan 'yan sanda yankin Mandera, Jeremiah Kosiom, ya tabbatar da kisan dan sandan sa kai 1 da dan kungiyar al-Shabaab 1. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China