Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana samun karuwar masu amfani da hidimomin wayar salula a Kenya
2019-12-24 09:28:02        cri

Wani rahoto da hukuma mai lura da harkokin sadarwa ta kasar Kenya ko CA ta fitar, ya nuna karuwar masu amfani da hidimomin layukan wayar salula a kasar.

Rahoton ya ce karuwar sabbin hidimomi da kamfanonin sadarwa ke samarwa, ya sanya 'yan kasar da dama mallakar layin waya fiye da guda daya domin more hidimomi daban daban.

Hukumar CA ta ce, a yanzu haka adadin karuwar hidimomin wayar salula a kasar ya kai kaso 112 bisa dari. Alkaluman da ke kunshe cikin rahoton wanda aka fitar a jiya Litinin, sun nuna cewa tsakanin watannin Yuli zuwa Satumbar wannan shekara ta 2019, adadin masu amfani da layukan salula a Kenya ya kai mutane miliyan 53.2.

A daya hannun kuma, yawan al'ummar kasar masu amfani da hidimomin shiga yanar gizo na 2G ya kai kaso 96 bisa dari, kana yawan masu amfani da fasahar 3G ya kai kaso 93 bisa dari.

A 'yan shekarun baya bayan nan dai, hukumar ta CA na ci gaba da bullo da karin matakan fadada hidimomin yanar gizo zuwa dukkanin sassan kasar, matakan da suka hada da tabbatar da cewa, kamfanonin dake samar da wannan hidima na bin dokoki yadda ya kamata, da kuma samar da karin lasisi ga kamfanonin dake iya samar da hidimar wayar salula.

Bugu da kari, an samar da damar amfani da hidimomin wayoyin tafi da gidan ka tsakanin kasa da kasa, musamman tsakanin Kenya da kasashe mambobin kungiyar raya gabashin Afirka ta EAC, kasashen da kuma ke yanki guda ta fuskar wannan hidima, kana suke cin gajiya daga hidimomi masu arha, wadanda suka hada da Uganda, da Sudan ta kudu da kuma Rwanda.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China