Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya ta dauki nauyin taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin makamashi
2019-12-14 16:32:39        cri

A jiya Juma'a Kenya ta karbi bakuncin taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika a fannin makamashi karkashi shawarar ziri daya da hanya daya (BRI).

Dandalin, shi ne irinsa na farko da wata cibiyar kwararrun kasashen Afrika (API) dake Nairobi, tare da hadin gwiwar cibiyar kula da albarkatun man fetur da nazarin fasahohi ta kasar Sin (CNPC ETRI), wato wata babbar cibiyar nazarin albarkatun mai ta kasar Sin mafi girma suka shirya.

Taron wanda ya samu halartar jakadun kasashen Afrika, da masana tsara dabarun ci gaba, da shugabannin kamfanoni, da kwararrun masana, ya tattauna game da muhimman damammakin da ake da su a fannin kasuwannin kamamashi a Afrika, damammakin da za su iya taimakawa wajen bunkasa cigaban nahiyar baki daya.

Wu Peng, jakadan kasar Sin a Kenya, ya ce kasarsa a shirye take ta taimaka wajen bunkasa fannin makamashi a Afrika karkashin manufofin shawarar ziri daya da hanya daya.

Jakada Wu ya ce, ana gudanar da hadin gwiwa a fannin makamashi ne karkashin tsari na moriyar juna tsakanin Sin da Afrika. Kamfanonin kasar Sin a shirye suke su shiga kasuwannin makamashin Afrika, kamar bangaren samar da makamashi ta hanyar iska zuwa mai amfani da hasken rana.

Ya ce kasar Sin ta taimaka wajen bunkasa ci gaban fannonin albarkatun man fetur da iskar gas a kasashen Afrika da dama, tare kuma da sayen albarkatun domin karfafa gwiwar tsarin yin takarar ciniki don bunkasa tattalin arzikin nahiyar.

Peter Kagwanja, babban jami'in cibiyar API, ya ce akwai bukatar gaggawa na shirya tattaunawa tsakanin Sin da Afrika game da batun bunkasa dangantaka tsakanin sassan biyu a fannin makamashi karkashin shawarar ziri daya da hanya daya.

Kagwanja ya ce, Afrika tana matukar bukatar yin hadin gwiwa da Sin domin cike gibi a fannin makamashi a nahiyar Afirka, inda a halin yanzu kusan kashi 50 bisa 100 na al'ummar ba su samun damar amfani da lantarki.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China