![]() |
|
2019-08-14 09:08:13 cri |
Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya yi gargadin cewa, an samu karuwar keta hakkokin yara a Mali a bana, musammam ta hanyar kashe su da azabtarwa.
Kwarya kwaryar bayanai da MDD ta samu sun nuna cewa, sama da yara 150 ne aka kashe a rikice-rikice a Mali cikin rabin farko na bana, idan aka kwatanta da 77 na bara.
Baya ga haka, wasu 75 sun ji rauni sanadiyyar rikice-rikicen, adadin da ya dara 24 na makamancin lokacin a bara. Raunikan sun hada da na harbin bindiga da kuna da karaya.
A cewar rahoton UNICEF, horarwa da amfani da yara da kungiyoyi masu dauke da makamai ke yi ya rubanya, inda a bana aka horar da yara 99, adadin da ya zarce 47 na makamancin lokacin a bara.
UNICEF ta ce wadannan adadi, sun nuna mummunan tasiri dadewar rashin tsaro a yankin arewacin kasar da kuma tabarbarewarsa a yankin tsakiyar kasar, da kuma iyakokin kasar da kasashen Niger da Burkina Faso. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China