Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kara tasoshin 5G 13,000 a birnin Beijing
2020-06-11 10:16:03        cri

Mahukuntan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, sun ce nan da karshen wannan shekara ta 2020, za a gina karin tasoshin fasahar sadarwa na 5G har 13,000, a wani mataki na bunkasa samar da ababen more rayuwa.

Bisa tsarin aiki a wannan fannin na shekarar 2020 zuwa 2022, za a gaggauta gina sabbin ababen more rayuwa da dama, inda ake sa ran zuwa karshen shekarar bana, za a kammala gina tasoshin 5G da jimillar yawan su zai kai 30,000 a birnin na Beijing.

Har ila yau, ta amfani da fasahohin "5G plus VR da AR", birnin na Beijing zai goyi bayan samar da hidimomin amfani da shagunan yanar gizo na kai tsaye, za a kuma sauya hidimomin sadarwa da za a yi amfani da su yayin gasar wasannin Olympics na birnin Beijing na lokacin sanyi a shekarar 2022, ta yadda hidimomin za su dace da fasahar 5G. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China