Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gina tasoshin 5G sama da dubu 130 a bara
2020-01-20 19:56:37        cri

Yau a nan birnin Beijing ministan ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin Miao Wei ya bayyana cewa, tatttalin arzikin masana'antun kasar ya gudana yadda ya kamata a shekarar 2019 da ta gabata, adadin kudin shigar manyan kamfanonin kasar ya karu da kaso 5.7 bisa dari, wanda ya dace da hasashen da aka yi.

Rahotanni sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2019, gaba daya adadin wayoyin salula masu fasahar 5G da aka sayar a kasuwar kasar ya zarta miliyan 13 da dubu 770, kuma an fara yin amfani da fasahar 5G a wayoyin salula da kasar Sin ta kera a bangaren kasuwanci. Minista Miao Wei ya ce, bana kasar Sin za ta kara sa kaimi kan aikin amfani da 5G a sana'o'i daban daban.

Jami'in ya kara da cewa, har kullum kasar Sin tana maraba da kamfanonin waje da su shiga aikin raya fasahar 5G a kasar, bisa dokokin da abin ya shafa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China