Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta raya birane masu amfani da fasahohin sadarwa kamar 5G
2019-11-29 15:52:55        cri

Bisa labarin da ma'aikatar harkokin masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ta bayar a ranar 29 ga wata, Sin za ta raya fasahohin sadarwa kamar fasahar 5G, da yanar gizo ta masana'antu da sauransu, don raya sha'anin bada hidima, da raya sabbin tsare-tsare da sha'anoni, ciki har da harkar sufuri mai amfani da fasahohin zamani da sauransu, don samar da gudummawa wajen raya birane.

Gaggauta raya birane da warware matsalolin da aka kawo yayin da ake raya birane ta hanyar fasahohin sadarwa, ya biya bukatun raya birane mai dorewa, da kuma kasancewa sabon karfi wajen raya sana'o'i. A halin yanzu, ana kokarin raya birane masu amfani da fasahohin sadarwa, da kawo sauki ga sha'anin bada hidima. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China