Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin: Sin na son ci gaba da hadin gwiwa da EU wajen tinkarar cutar coronavirus
2020-02-12 20:57:03        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Mr. Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasar Sin na godiya ga kasa da kasa, ciki hadda kungiyar tarayyar Turai, bisa tallafi da taimakon da suka baiwa kasar Sin, kuma tana son ci gaba da mu'amala da hadin gwiwa da kasa da kasa, ciki har da hukumar lafiya ta duniya, don tinkarar cutar cikin hadin gwiwa. Geng Shuang ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka shirya a yau Laraba ta yanar gizo.

Rahotanni na cewa, ministocin kiwon lafiya na kasashe 27 na kungiyar tarayyar Turai, za su shirya taron musamman a gobe Alhamis, dangane da cutar. A watan da ya gabata kuma, kungiyar ta ware dalar Amurka miliyan 10, domin nazarin cutar, kuma za ta ci gaba da samar da gudummawa ga kasar Sin wajen dakile yaduwarta. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China