Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Burundi ya mutu sanadiyyar bugun zuciya
2020-06-10 10:48:25        cri

Pierre Nkurunziza, shugaban kasar Burundi ya mutu a sakamakon bugun zuciya a wani asibiti dake shiyyar gabas ta tsakiyar kasar, wata sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar a ranar Talata ta tabbatar da mutuwar shugaban.

Sanarwar ta ce, Nkurunziza ya kalli wasan kwallo a lardin Ngozi da yammacin ranar 6 ga watan, kafin daga bisani aka garzaya da shi zuwa wani asibiti dake lardin Karusi domin duba lafiyarsa bayan da ya fara jin rashin lafiyar da yammacin wannan rana.

Daga bisani yanayin lafiyarsa ta inganta a ranar Lahadi, amma abin mamaki daga baya al'amurra sun sauya, ya mutu yana da shekaru 55 a duniya, sanarwar ta kara da cewa, wata tawagar kwararrun likitoci sun shafe sa'o'i suna kokarin ceto rayuwarsa, amma lamarin ya faskara daga bisani ya rasu.

Sanarwar ta ce, gwamnatin kasar Burundi ta yiwa iyalan marigayin ta'aziyya tare da sauran dukkan mutanen kasar Burundin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China