Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta taya sabon zababben shugaban Burundi murnar lashe zabe
2020-06-05 19:57:19        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce Sin na taya sabon zababben shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye, murnar lashe zaben kasar da aka gudanar.

Geng Shuang, ya gabatar da sakon taya murnar ne a Juma'ar nan, yayin taron manema labarai na rana rana da ake gudanarwa a nan birnin Beijing, inda ya ce Sin a shirye take, ta yi aiki tare da Burundi, wajen daga matsayin dangantakar sassan biyu zuwa wani sabon matsayi.

A jiya Alhamis ne dai kotun tsarin mulki ta Burundi, ta sanar da sakamakon zaben shugabancin kasar. Inda ta ayyana Mr. Ndayishimiye, na jam'iyya mai mulkin kasar, a matsayin wanda ya lashe zaben.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China