![]() |
|
2020-06-10 10:27:39 cri |
A ranar Talata Najeriya ta gabatar da sunan Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin wacce za ta shugabanci hukumar cinikayya ta duniya WTO, wata sanarwar hukumar WTO ce ta bayyana hakan.
Bayanin tarihin da WTO ta wallafa a shafin intanet ya nuna cewa, Okonjo-Iweala kwararriya ce a fannin harkokin kudi da tattalin arziki ta kasa da kasa, kuma tana da kwarewar aiki a fannin hada hahar kudade a matakin kasa da kasa na sama da shekaru 30 inda ta yi aiki a fannonim kudi daban daban a duniya.
Ta taba rike ministar kudi a Najeriya har karo biyu, kana ta taba rike mukamin ministar harkokin waje na takaitaccen lokaci, ta shafe shekaru 25 tana aiki a bankin duniya, ta rike mukamin manajan daraktar gudanarwar bankin duniyar. A yanzu haka ita ce ke shugabantar hukumar Gavi dake kula da aikin samar da allurar rigakafi, a kwanan nan an nada ta a matsayin wakiliyar musamman ta kungiyar AU domin jagorantar asusun tattara kudaden yaki da annobar COVID-19 ta kasa da kasa.
A cikin bayanin tarihinta, Okonjo-Iweala kwararriya ce a fannin shiga tsakani, ta kware a fannin cimma daidaito, kuma mai gaskiya da rikon amana ce wajen tafiyar da harkokin kudade, hakan ya ja hankalin gwamnatoci da masu ruwa da tsaki wajen amincewa da ita a matakai daban daban na kasa da kasa.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China