Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 6 sun mutu wasu 6 sun ji rauni a hadarin mota a kudancin Najeriya
2020-06-10 10:01:59        cri

Yan sandan Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 6 a lokacin da wata babbar motar daukar kaya ta fadi kan babura masu kafa uku da kananan motocin bus a birnin Onitsha dake shiyyar kudu maso gabashin Najeriya da safiyar ranar Talata.

Babbar motar wacce direban ya kasa sarrafa ta, a yankin Upper Iweka, a birnin Onitsha dake jihar Anambra, kuma gangar jikin motar wacce kwantina ce ta fada kan babura masu kafa uku kimanin shida da wasu kananan motocin bus biyu, a cewar Haruna Mohammed, kakakin hukumar 'yan sandan jihar.

Mohammed ya ce, jami'an aikin ceto sun shafe sa'o'i suna gudanar da aiki, lamarin da ya yi sanadiyyar cunkoson ababen hawa a yankin mai fama da yawan zirga zirgar jama'a. An kwashe gawarwakin mutanen da suka mutu da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti dake yankin.

Ya ce jami'an 'yan sanda suna ci gaba da gudanar da bincike game da hadarin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China