Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar tuntuba ta Arewacin Najeriya ta damu game da yawaitar fyade a yankin
2020-06-10 09:57:06        cri

Kungiyar tuntuba ta Arewacin Najeriya ko ACF, ta bayyana matukar damuwa, game da yawaitar aikata fyade a yankin. Kakakin kungiyar Emmanuel Yawe, wanda ya yi Allah wadai da hakan cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafi, ya ce muggan ayyuka na neman zama ruwan dare a yankin na arewacin Najeriya.

Yawe wanda ya tabbatar da karuwar laifin fyade a yankin, ya yi kira ga iyaye, da masu kula da yara, da 'yan mata, da masu kula da makarantu, da malaman addini, da su maida hankali wajen daukar matakan dakile wannan mummunan laifi na rashin da'a.

Daga nan sai ya yi kira ga mahukunta a kasar, da su bullo da karin matakan hukunta masu aikata fyade, ta hanyar tsaurara dokoki na dakile wannan mummunar ta'ada. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China