Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun Nijeriya sun matse kaimi a yaki da kungiyar BH
2020-06-06 16:29:13        cri

Dakarun Nijeriya na samun kyawawan sakamako a ayyukan da suke na yaki da kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan bindiga dake yankin arewacin kasar.

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar, John Enenche, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya cewa, an kashe gomman mayakan kungiyar, yayin da wasu da dama suka mika wuya ga dakarun tsakanin ranekun Litinin da Laraba.

Ya ce a ci gaba da ake da ayyukan fatattakar 'yan tada kayar baya a yankin arewa maso gabashin kasar, rundunar Super Camp 6 da hadin gwiwar kungiyar tsaro ta Civilian JTF, sun kaddamar da wani harin kwantar bauna a ranar Laraba, a yankin kogin Lawanti na garin Konduga dake jihar Borno, inda suka kashe mayakan BH 6, yayin da sauran suka tsere da raunikan bindiga.

Ya kara da cewa, ko a ranar Talata, dakarun sun yi arangama da wasu mayakan BH a Daban Magaji dake jihar Borno, lamarin da ya kai ga kisan 9 daga cikin mayakan da kuma lalata tankar yaki guda ta kungiyar tare da kwato bindigar kakkabo jirgi da wasu bindigogi 2 da kuma tarin wasu makamai.

Ya ce dakarun za su ci gaba da zage damtse wajen yaki da kungiyar BH da sauran kungiyoyin masu dauke da makamai. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China