Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Da dace Birtaniya ta martaba ikon Sin na wanzar da tsaro a yankin HK
2020-06-09 10:39:17        cri

Dan majalissar gudanarwar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana fatan ganin Birtaniya ta martaba ikon halas na kasar Sin, na wanzar da tsaro a yankin Hong Kong.

Wang Yi ya yi wannan fata ne a jiya Litinin, yayin tattaunawa ta wayar tarho da sakataren wajen Birtaniya Dominic Raab. Ya ce batun Hong Kong magana ce ta cikin gidan kasar Sin, wanda ba wani bangare na waje dake da hurumin tsoma hannu cikin sa. Ya ce tabbatar da tsaron yankin Hong Kong ya shafi muhimmiyar moriyar kasar Sin, don haka batu ne na akidar kasar da wajibi ne a kare shi.

Wang ya kuma jaddada cewa, dalilin kafa dokar tsaro mai nasaba da yankin Hong Kong shi ne, tabbatar da gudanar da salon mulkin "kasa daya amma tsarin mulki biyu". Ya kuma ce sashe na daya na dokar da majalissar wakilan jama'ar Sin ta NPC ta amince da shi, ya bayyana a fili cewa, za a martaba salon mulkin "kasa daya, tsarin mulki biyu," ta yadda "Al'ummar Hong Kong za su jagoranci Hong Kong", tare da samar da 'yanci mai ma'ana ga yankin.

Wang ya kara da cewa, dokar tsaro mai nasaba da yankin Hong Kong, za ta yi aiki ne kan wasu tsiraru dake rajin "Samar da 'yancin mulkin kai, da 'yan aware, da masu tada kayar baya. Kana dokar za ta tabbatar da kare hakkokin al'ummun yankin na Hong Kong, za ta kuma baiwa baki 'yan kasashen waje mazauna yankin kyakkyawan yanayi, na aiki, tare da rayuwa cikin kwanciyar hankali.

Ya ce a matsayin su na mambobin din din din a kwamitin tsaron MDD, ya dace Sin da Birtaniya sun nuna kyakkyawan misali, na martaba dokoki, da alakar kasa da kasa, su kuma kaucewa tsoma baki a harkokin cikin gidan juna. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China