Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan jami'ai da kwararrun kasashen Afirka da dama suna goyon bayan kudurin Sin kan HK
2020-06-04 18:49:26        cri

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, manyan jami'ai da kwararru na kasashen Afirka da dama, sun nuna goyon bayansu ga kudurin dake shafar tsaron Hong Kong, yankin musamman na kasar Sin da aka zartas, a yayin babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.

Sassan sun bayyana cewa, kudurin da aka zartas ya nuna cewa, kasar Sin ta samu ci gaba, yayin da take kafa dokar tsaro a yankin Hong Kong, kuma ko shakka ba bu, hakan zai kara karfafawa bangarori daban daban na yankin gwiwa, yayin da suke kokarin farfado da tattalin arziki a yankin.

A ranar 2 ga wata, sabon shugaban majalisar dokokin kasar Mali Musa Thimbine ya bayyana cewa, harkar yankin Hong Kong harkar cikin gida ce ta kasar Sin, don haka bai kamata sauran kasashen duniya, su tsoma baki a cikin ta ba, kuma kasar Mali za ta ci gaba da goyon bayan ikon mulkin kasa, da cikakken yankin kasa na Sin, kana za ta ci gaba da goyon bayan manufar kasar Sin ta "kasa daya mai tsarin mulki iri biyu", haka kuma za ta ci gaba da goyon bayan yunkurin kasar Sin, na tabbatar da wadata da zaman lafiya a yankin Hong Kong.

Kafin hakan a ranar 1 ga wata, wani masanin siyasar kasa da kasa da manufofin harkokin diplomasiyya, a jami'ar Obafermi Avolovo dake tarayyar Najeriya Mr. Allad Fowler, ya wallafa wani rahoto a jaridar The Nation, inda ya tono mugun yunkurin kasashen yamma, da wasu kafofin watsa labarai na kasashen, kan batun yankin Hong Kong, kana ya yi nuni da cewa, ba zai yiwu, wadanda ke tayar da tarzoma a yankin, su samu goyon baya daga kasashen yamma ba.

Har ila yau a ranar 2 ga watan nan, kakakin gwamnatin Uganda, Ofwono Opondo, ya bayyana cewa, ya dace a daidaita harkokin kasar Sin bisa tsarin dokokin kasar, kuma bai kamata wasu kasashen duniya su tsoma baki a cikin wannan batu ba. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China