Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakan da ake aiwatarwa game da HK za su kare moriyar yankin
2020-06-04 19:46:09        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce dukkanin matakan da ake aiwatarwa game da Hong Kong, na da matukar alfanu ga ci gaban yankin.

Zhao Lijian, wanda ya bayyana hakan, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa, ya ce kudurorin da majalissar wakilan jama'ar kasar Sin ta tsara, da ma matakai na gaba, na kafa dokoki, wadanda zaunannen kwamitin majalissar zai aiwatar, za su taimaka wajen kare ikon mulkin kai, da tsaro, da ci gaban kasar Sin baki daya.

Kaza lika, hakan zai tabbatar da daidaito na tsawon lokaci, da ci gaba a yankin na Hong Kong, kana dai wanzar da damar aiwatar da salon "kasa daya, tsarin mulki biyu ", wanda baya ga kare moriyar yankin na Hong Kong, zai kuma tabbatar da kare moriyar sassan kasa da kasa dake cudanya da yankin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China