2020-06-09 09:35:35 cri |
Bankin duniya ya yi hasashen raguwar tattalin arzikin duniya da kaso 5.2 bisa dari a wannan shekara ta 2020, sakamakon fama da ake yi da yaduwar cutar COVID-19, komadar da za ta kasance mafi tsanani da tattalin arzikin duniyar zai fuskanta, tun bayan yakin duniya na biyu.
Wani rahoto da bankin ya fitar game da hakan a jiya Litinin, ya ce hada hadar tattalin arzikin kasashe masu wadata za ta ragu, da kaso 7 bisa dari a bana, yayin da bukatar hajoji, da cinikayya, da sauran harkokin kudade suka tsaya cik.
Rahoton ya ce a shekarar ta bana, tattalin arzikin Amurka zai ragu da kaso 6.1 bisa dari, yayin da na yankin Turai zai ragu da kaso 9.1 bisa dari. Sai na sassan kasashe da tattalin arzikin su ke saurin bunkasuwa, da na kasashe masu tasowa, wanda zai ragu da kaso 2.5. Wannan ne dai karo na farko da a jimlace, tattalin arzikin wadannan yankuna zai yi kasa, tun bayan kusan shekaru 60 da suka gabata.
A daya bangaren kuma, harkokin tattalin arzikin kasashen Latin Amurka, da ma musamman na Caribbean, zai iya fuskantar raguwar da ta kai ta kaso 7.2 bisa dari a wannan shekara ta 2020.
A bangaren gabashin Asiya da yankin Pacific kuwa, kasashen yankin za su samu raguwa da ba ta wuce kaso 0.5 bisa dari ba a shekarar ta bana, wanda hakan ke nuna cewa, mai yiwuwa yankin ne kadai zai iya samun ci gaba a bana. Kaza lika akwai hasashen ci gaban kasar Sin, zai kai kaso 1 bisa dari a shekarar.
Kudaden shiga na al'ummu idan an kwatanta da jimillar tattalin arzikin kasashen su kuwa, shi ma an yi hasashen zai ragu da kusan kaso 3.6 bisa dari, matakin da mai yiwuwa ne ya jefa miliyoyin al'ummun duniya cikin matsanancin hali na talauci. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China