Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNECA ta ce za ta ba da fifiko wajen bunkasa yankin Sahel
2019-07-03 10:37:43        cri

Hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), ta sanar a jiya Talata cewa, yankin Sahel shi ne bangaren da MDD za ta fi baiwa fifiko karkashin shirinta na bunkasa ci gaban nahiyar Afrika.

Babban daraktan hukumar ECA na yammacin Afrika, Bakary Dosso, ya bayyana cewa, muhimman ayyukan da ECA ke gudanarwa a halin yanzu za su karkata ne ga yankin Sahel a matsayin shiyyar da za ta fi baiwa fifiko wajen cimma nasarar shirin samar da dawwamamman ci gaban nahiyar Afrika na (SDGs).

Daraktan na ECA, wanda ya jaddada bukatar a samar da wani tsarin hadin gwiwa na yunkurin samar da ci gaba da kuma matakan shawo kan kalubalolin tsaro a fadin yankin na Sahel, ya nanata cewa, irin halin da ake ciki na yawan tashe tashe hankula a yankin Sahel ba shi ne ke zayyana cikakken yanayin da ake ciki a shiyyar ba.

A cewar Dosso, sakatare janar na MDD ya umarci hukumar ECA da ta gudanar da nazari domin gano ainihin tushen abubuwan dake haifar da matsalolin da suke faruwa a shiyyar da kuma yadda za'a kafa wani muhimmin tsarin kawo sauyi a yankin.

ECA ta nanata muhimmancin dake tattare da tsarin bincike a yankin Sahel nan da shekarar 2043, wanda yana daya daga cikin tsare tsaren da MDD ta bullo da su da nufin tabbatar da samun hadin gwiwa tsakanin ayyukan raya ci gaba da yaki da ayyukan ta'addanci domin tabbatar da samun dawwamamman zaman lafiya a yankin Sahel baki daya.

ECA ta kuma bayyana bukatar aiwatar da shirin nazari na dogon zango, wanda kawo yanzu ya samu goyon bayan kasashe 10 na yankin Sahel da suka hada da Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Gambia, Guinea, Mali, Mauritania, Nijer, Najeriya, da Senegal.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China