Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lauyan iyalan Floyd ya ce annobar nuna wariyar launin fata ce ta yi sanadin Floyd
2020-06-05 10:32:48        cri

Lauyan iyalan marigayi George Floyd da wani dan sanda ya makure wuyansu da gwiwar kafarsa har ya sheka barzahu, Benjamin Crump, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, annobar nuna wariyar launin fata ce ta yi sanadiyar mutuwar bakar fatan.

Crump wanda ya bayyana haka, yayin jana'izar Floyd da aka shirya tun bayan kisan gillar da aka yiwa masa, ya ce, annobar nuna wariyar launin fata da kyama da muke gani a Amurka ce ta halaka George Floyd.

Lauyan ya ce, Amurka ba ta bukatar tsarin shari'a guda biyu, na bakaken fata da na farare. Kalaman nasa na zuwa ne, gabanin sanar da hukuncin da aka yankewa 'yan sanda da ake zargi suna da hannu a mutuwar Floyd.

Ya ce, abin da ko wane Ba-Amurke ke bukata, shi ne samun daidaito a kasar.

Jama'a da dama ne dai da suka hada da iyalan marigayi Floyd, da masu rajin kare hakkin bil-Adam, da jami'an jihar Minnesota da 'yan majalisar dokokin tarayya da suka hada da Senata Amy Klobuchar da 'yar majalisar wakilai IIhan Omar da wasu fitattun mutane ne, suka halarci jana'izar farko da aka shiryawa gawar Floyd, a babban dakin taron jami'ar North Central dake tsakiyar birnin Minneapolis, inda wasu 'yan sanda hudu suka kashe shi, don sake tuna kisan rashin adalcin da ake yi a kasar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China