Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na taimakawa wajen samar da rigakafi mai sauki a kasashe masu tasowa
2020-06-04 19:30:14        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin na taimakawa wajen samar da alluran rigakafi mai sauki a kasashe masu tasowa, tana kuma yayata gina tsarin kiwon lafiyar al'umma mai nagarta.

Kalaman na Zhao na zuwa ne, gabanin taron kasa da kasa game da alluran rigakafi, wanda aka tsara gudanarwa ta kafar bidiyo, da yammacin Alhamis din nan 4 ga wata, bisa agogon Beijing.

Ana kuma sa ran firaministan Sin Li Keqiang, zai gabatar da jawabi a yayin taron. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China