Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka ta yi watsi da matakan nuna wariyar launin fata
2020-06-01 21:14:25        cri

Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta yi kira ga kasar Amurka, da ta yi watsi da duk wasu matakai na nuna wariyar launin fata, ta kuma kare 'yancin al'ummun ta marasa rinjaye. Ma'aikatar ta ce ya kamata a kare hakkin dan Adam da rayukan bakaken fata.

Da yake tsokaci game da hakan ga manema labarai, mai magana da yawun ma'aikatar Zhao Lijian, ya ce muryar 'yan Afirka na kunshe da amincewa ta bai daya kan wannan muhimmin sako. Zhao ya kara da cewa, Sin na fatan Amurka za ta saurari manufarta, ta goyon bayan al'ummun Afirka.

Ya ce Sin za ta yi aiki da nahiyar Afirka, wajen yakar dukkanin wani nau'in nuna wariyar launin fata, da rura wutar nuna kyama da kiyayya.

A daya bangaren kuma, wata sanarwa ta yanar gizo da shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Musa Faki Mahamat ya fitar, ta yi kakkausan suka game da kisan matashin nan bakar fata George Floyd a Amurka, kuma a hannun jami'an tsaro da ya dace a ce su ne masu kare rayukan al'umma." (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China