Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira da a samar da tallafin kudade da na siyasa ga WHO bayan janyewar Amurka
2020-06-01 20:46:35        cri

Ma'aikatar wajen kasar Sin, ta yi kira ga kasashe mambobin hukumar lafiya ta duniya WHO, da su agazawa hukumar da tallafin kudade da goyon baya ta fuskar siyasa, biyowa bayan yanke hulda da Amurka ta ce ta yi da hukumar, sakamakon yadda WHO ta gudanar da ayyukan ta na yaki da cutar COVID-19.

Kakakin ma'aikatar Zhao Lijian, shi ne ya yi wannan kira a yau Litinin, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa. Zhao Lijian ya ce sassan kasa da kasa sun sabawa ra'ayin Amurka na nuna son kai. Inda ya ce Amurka ta saba da halayyar ficewa daga muhimman hukumomin kasa da kasa.

Ya ce WHO na da mambobi kasashe masu 'yanci har 194, kuma ba wata kasa guda take yiwa aiki ba, ba kuma za ta mika wuya ga wata kasa guda don kawai tana samar mata da kudade mafiya yawa ba.

Daga nan sai ya jaddada matsayin kasar Sin na kasancewa mai mutunci a ko da yaushe, wadda kuma za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan hukumar WHO, na hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da wannan cuta ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China