Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Essex: Bai kamata a siyasantar da rayuwar jama'a ba
2019-10-30 19:36:00        cri

Yayin da 'yan sandan Burtaniya ke ci gaba da gudanar da bincike game da gawarwakin mutane 39 da aka gano a cikin wata babbar mota a makon da ya gabata a Essex, a hannun guda kuma jama'a da dama na saka ayar tambaya kan jita-jitar da wasu kafofin watsa labarai suka watsa, dangane da asalin mamatan. Domin yana da kyau a rika sanar da duniya a kai a kai abubuwan dake gudana a zahiri, saboda babu wanda ya wuce yin kuskure. Amma, akwai kuskuren ganganci na 'yan jarida da ba za a amince shi ba. Duk abin da ka fada a cikin rahotanninka, labarai ne ko ra'ayi ya kamata ya fara da gamsassun shaidu.

'Yan sandan Exxes, sun fada a ranar Alhamis da ta gabata cewa, dukkan mamatan, an yi imanin Sinawa ne, amma, nan da nan suka janye sanarwar da suka bayar, sannan suka yi gargadi cewa a guji yada jita-jita.

A wani rahoto da aka watsa a gidan talabijin na Burtaniya, wakilinsu ya ce, 'yan sanda ba su tabbatar da cewa, mamatan Sinawa ba ne, ya dai ce labari ne daga wata kafa. Amma hakan bai hana shi tuna abin da aka fada a baya cewa, akwai Sinawa a ciki ba. Haka kuma a wata kafar yada labaran, wata babbar mai gabatar da shiri, ta tunatar da masu kallon tashar cewa, ba a tabbatar da cewa Sinawa ne a cikin babbar motar ba. Amma ta bayyana cewa,, "Mu kaddara haka ne" har ma ta tambayi bakon da take hira da shi, kan ya yi sharhi kan yadda mahukuntan kasar Sin ka iya musgunawa iyalan mamatan idan suka fito fili su bayyana cewa, 'yan uwansu na daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su.

Irin wadannan labarai, sun gamu da suka daga daukacin Sinawa. Wakilan kafofin watsa labarai da dama na ketare, sun yi ta kokarin jin ta bakin al'ummar Sinawata, kan yadda za su bayyana abin da suka yi imani ba haka ba ne don ya zama gaskiya. Amma, bai kamata a yi riga malam masallaci ba. Hakan na iya bata aikin jarida.

A yayin da 'yan sanda ke ci gaba da gudanar da bincike don gano gaskiyar lamari, kamata ya yi mu jira, mu kuma yi tunani kan makomar wadanda suka riga mu gidan gaskiya. Domin sun cancanci a mutunta su.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China