Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da babban zaben Birtaniya
2019-11-07 10:31:50        cri

A jiya Laraba aka kaddamar da gangamin yakin neman babban zaben kasar Birtaniya a hukumance bayan da firaminsitan kasar Boris Johnson ya yi wata ganawa da sarauniyar Ingila Elizabeth II domin neman amincewarta don rusa majalisar dokokin kasar.

Majalisun dokokin kasar sun rufe kofofinsu tun a tsakar dare kuma ba za su sake budewa ba sai bayan zaben na ranar 12 ga watan Disamba. Rusa majalisar ya ba da dama ga jam'iyyun siyasar kasar ci gaba da gangamin yakin neman zaben har zuwa ranar zaben inda masu jefa kuri'a a kasar sama da miliyan 46 za su kada kuri'unsu. Zaben zai kasance karo na uku na babban zaben Birtaniya cikin shekaru biyar, tun bayan zabukan da aka gudanar a 2015 da 2017.

A yayin da mista Johnson ke jagorantar gwamnati maras rinjaye da kuma makomar kasar Birtaniyan game da batun ficewar kasar daga tarayyar Turai, hakan zai iya kasancewa wani muhimmin al'amari ga masu zabe a kasar da kawunan 'yayanta suka rabu game da batun ficewar kasar daga tarayyar Turai, sakamakon zaben, shi ne zai tabbatar da makomar abin da zai faru ga aniyar mista Johnson kan batun yarjejeniyar ficewar Birtaniyar daga tarayyar Turai wanda wa'adin zai cika a ranar 31 ga watan Janairu shekarar 2020.

Johnson zai tafi zuwa yankin dake tsakiyar kasar Birtaniyan a daren Laraba domin kaddamar da gangamin yankin neman zaben jam'iyyar Conservative a hukumance.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China