Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Ana fatan kudin tallafi da Amurka ta bayar zai taimaka
2020-02-19 20:23:29        cri

Kwanan baya, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da baiwa wa Sin da sauran kasashe tallafin kudi da ba zai wuce dala miliyan 100 ba don fama da cutar numfashi ta COVID-19. Game da wannan batu, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya bayyana yau Laraba, cewa bangaren Sin na fatan tallafin zai taimaka wajen hanzarta kawar da cutar.

Ban da wannan kuma Geng ya ce, babu iyakar kasa a fannin yaki da annoba. Sin na maraba da ma godiya ga dukkan taimakon da kasashen duniya ciki har da Amurka ke bayarwa.

Geng ya kara da cewa, kwanan baya Amurka ta baiwa wa lardin Hubei na kasar Sin kayayyakin rigakafin cutar da nauyinsu ya kai tan 16, ciki har da abubuwan rufe baki da hanci, rigunan kariya, da na'urar samar da iskar numfashi da dai sauransu.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China