Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya aike sakon taya murnar ranar yara ta kasa da kasa
2020-05-31 16:17:29        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya yaran dukkan kabilun kasar Sin murnar zagayowar ranar yara ta kasa da kasa, wacce ta fado a ranar 1 ga watan Yuni.

Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na hukumar sojojin kasar Sin, ya yi kira ga kananan yara da su kara himma da kwazo wajen karatu, su maida hankali wajen gina kyakkyawan tunani, da lura da lafiyar jikinsu domin yin kyakkyawan tanadi wajen cimma burin al'ummar Sinawa na kawo sauye sauye masu ma'ana ga ci gaban kasa.

Xi ya jaddada cewa, yaran kasar Sin na wannan zamani ba kawai suna fuskantar lokacin cimma nasarorin da magabatan farko suka gina kasar a kai ba ne, har ma sun kasance a matsayin wani sabon karfi don cimma nasarori da kuma gina kasar Sin mai salon gurguzu na musamman a zamanin da muke ciki.

Shugaba Xi ya bukaci kwamitocin jam'iyya da gwamnatoci a dukkan matakai da ma al'umma baki daya da su kula da kananan yara, kana su samar da wani ingantaccen muhallin kyautata rayuwar kananan yara.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China