Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta aike da tawagogi 148 zuwa kasashen Afirka 11 don yaki da COVID-19
2020-06-02 19:41:00        cri

Ma'aikatar wajen kasar Sin, ta ce a yunkurin kasar na tallafawa kasashen nahiyar Afirka a yakin da suke yi da cutar numfashi ta COVID-19, Sin ta aike da tawagogin masana a fannin kiwon lafiya har 148, zuwa kasashen Afirka 11 bisa gayyatar kasashen.

Kakakin ma'aikatar wajen Sin din Zhao Lijian ne ya shaidawa manema labarai hakan, yayin taron ganawa da 'yan jaridu na rana rana da aka saba gudanarwa, na yau Talata a nan birnin Beijing.

Zhao Lijian ya ce, jami'an dake cikin tawagogin sun yi zuzzurfar tattaunawa da sassan masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya na kasashen da suka halarta, sun kuma gabatar da kwarewar su ga takwarorin na su a bangaren yaki da wannan annoba.

Kaza lika sun zanta da al'ummun kasashe, sun ziyarci wasu asibitoci da dakunan gwaji, kana sun nunawa jami'an lafiyar kasashen managartan dabarun yakar cutar, matakin da ya samu matukar yabo daga kasashen.

Game da yanayin ci gaba da aka samu, don gane da ginin cibiyar kandagarki, da yaki da cututtuka ta Afirka, Zhao Lijian ya ce Sin na dora matukar muhimmanci kan wannan aikin, tana kuma hadin gwiwa da kasashen nahiyar wajen tsara aikin aza tubalin ginin cibiyar, ba tare da wani bata lokaci ba, ta yadda aikin zai kai ga inganta harkokin kiwon lafiyar al'ummun nahiyar baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China