Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta nuna rashin jin dadi kan yadda Amurka ta mai da kafofin watsa labarai biyar nata a matsayin tawagogin jakadu dake Amurka
2020-02-19 20:18:48        cri

Kwanan baya, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta mai da hukumomin kafofin watsa labaran kasar Sin guda biyar da ke Amurka a matsayin tawagogin jakadun Sin da ke kasar, kuma ta bukace su da su yi rajistar ma'aikatansu da kadarorinsu da ke Amurka. Game da batun, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana yau Laraba, cewar Sin ta nuna matukar rashin jin dadinta da ma rashin amincewa da wannan mataki na Amurka da bai dace ba.

Geng ya kara da cewa, ko da yaushe hukumomin kafafin watsa labaran Sin da ke kasar Amurka na gudanar da aikin jarida bisa ka'idojin adalci da gaskiya da daidaito, sa'an nan tana taka rawar a zo a gani a fannin kara fahimta da cudanyar al'adu a tsakanin jama'ar Sin da Amurka.

Ban da wannan kuma Geng ya nuna cewa, ko da yaushe Amurka na daukar kanta a matsayin mai girmama 'yancin watsa labarai, amma ta kan kawo cikas ga hukumomin kafofin watsa labaran Sin da ke kasar. Gaskiya babu wata hujja ko kadan da ta daukar irin wannan mataki, wanda ba za a amince da shi ba. Don haka bangaren Sin ya kalubalanci Amurka da ta daina nuna bambancin ra'ayi ga kasar Sin, da ma kau da ra'ayin yin takara ba hadin gwiwa, da daina daukar matakan da ba su dace da za su iya raunata amincewa da hadin kan bangarorin biyu. Kasar Sin za ta kiyaye hakkinta na kara mayar da martani kan batun. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China