Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya: 'Yan bindiga sun hallaka wasu manyan jami'ai a jihar Katsina
2020-06-01 20:53:06        cri

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta shiga farautar wasu 'yan bindiga da suka hallaka wani jagoran jam'iyyar APC mai mulkin kasar a jihar Katsina dake arewa maso yammacin kasar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a Litinin din nan, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Gambo Isah, ya ce 'yan bindigar sun hallaka Abdulhamid Sani, shugaban jam'iyyar APC reshen karamar hukumar Batsari dake jihar ta Katsina ne a ranar Lahadin karshen mako, bayan da yunkurin su na yin garkuwa da shi ya ci tura.

A wata sanarwar ta daban kuma, Gambo Isah ya ce wasu gungun 'yan bindigar dauke da bindigogi kirar AK 47, sun kai hari garin Dan Musa da almurun ranar Lahadi, inda suka harbi hakimin karamar hukumar ta Dan Musa Abu Atiku, da wani dogarin sa.

Bayan garzayawa da su asibiti ne kuma, jami'an lafiya suka tabbatar da rasuwar hakimin, yayin da dogarin na sa ke ci gaba da samun kulawa a asibiti. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China