Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan bindiga sun kashe wasu sojoji biyu a Najeriya
2020-02-19 19:32:25        cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, wasu sojoji biyu sun gamu da ajalinsu, kana guda ya ji mummunan rauni, sakamakon wani hari da wasu 'yan bindiga da ake zaton makiyaya ne suka kaddamar a yankin Barkin Ladi na jihar Filato dake yankin arewa maso tsakiyar Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Filato Obah Ogaba, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos, babban birnin jihar faruwar lamarin, ya bayyana cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ce, 'yan bindiga sun yiwa jami'an tsaron sashe na biyar kwanton bauna, inda suka kashe sojoji biyu, tare da jikkata guda, kuma wannan abin damuwa ne matuka.

Sai dai kuma wata majiyar tsaro ta kara da cewa, wasu sojoji da suka fusaka da faruwar lamarin, sun baiwa mazauna wurin wa'adin kwanaki biyu, kan su fito da mahara, inda aka yi zargin cewa, sun mamaye garin a ranar Talata suka kuma bankawa gidaje da dama wuta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China