Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnati ta damu kan yawaitar hare haren 'yan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya
2020-05-31 16:55:05        cri

Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa da takaici sakamakon yawaitar hare haren 'yan bindiga a shiyyar arewa maso yammacin kasar, wanda ya yi sanadiyyar gwamman rayukan fararen hula.

Ministan al'amurran 'yan sanda na Najeriyar, Muhammad Dingyadi, ya bayyana aniyar gwamnatin kasar ta kawo karshen matsalolin tsaro dake addabar shiyyar arewa maso yammacin kasar, inda a 'yan shekarun baya bayan nan ake ta samun yawaitar hare haren bata gari wanda ya hada da barayin shanu da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

A watan Fabrairu, dakarun tsaron Najeriya sun kaddamar da wani gagarumin shiri da nufin murkushe hare haren 'yan bindiga a shiyyar arewacin kasar.

Aikin sintirin, a cewar ministan 'yan sandan, an kaddamar da shi ne don kawar da dukkan nau'ikan ayyukan 'yan bindiga a shiyyar domin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.

Ya ce, aikin sindirin ya haifar da kyakkyawan sakamako wajen dakile hare haren barayin shanu da tarwatsa maboyar 'yan bindigar a yankunan.

Da yake tsokaci game da hare haren, Chukwuma Okoli, wani malami kuma mai nazari kan al'amurran yau da kullum na jami'ar gwamnatin tarayyar ta Lafia, ya ce, yunkurin gwamnatin tarayya na baya bayan nan don yaki da 'yan bindigar, bisa ga irin hare haren da sojoji ke kaddamarwa, ana samun kyakkyawan sakamakon wanda ya cancanci yabo.

Kwararren masanin kimiyyar siyasar ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ya kamata a samar da tsarin jami'an tsaro na kananan yankuna, wadanda za su gudanar da aikin hadin gwiwa tare da mazauna yankunan wajen aikin tattara bayanan sirri.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China